Matsalar Dokar Hana Barace-Barace a Jihar Kano

Wasu nakasassu a Kano.

Kwana kwanan nan gwamnatin jihar Kano ta kafa dokar hana barace-barace to sai dai daga fannin shari'a da ma kundin tsarin mulkin kasar Najeriya, da alama dokar tana da matsala
Jihar Kano ta kafa dokar hana bara a jihar amma masana shari'a sun ce dokar zata yi wuyar aiwatarwa domin wasu dalilai.

A shari'ance wai dokar tana da wasu gibuka. Na daya an yi dokar ne da nufin hana barace-barace kan tituna. To amma babu inda dokar ta bayyana abun da take nufi da bara kan tituna. Idan mutum ya shiga inda ba titi ba ne yana bara shin wannan doka zata kamashi? Abu na biyu, sashe na 36 karamin layi na 12 cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya ce lalle ne a samu doka kuma dokar ta fayyace cewa abu kaza shi ne laifi.Sai ta fayyace laifin kana kuma ta fadi hukuncin da za'a yi.

Dokar yadda take yanzu ta fadi hukunci ne amma bata fayyace abun da ake nufi da bara kan tituna ba. Abu na biye da wannan shi ne tsarin gudanar da majalisar dokokin Kano ya ce kafin kakakin majalisar ya bari a gabatar da wani kudiri ko doka da zata shafi wani ko wasu ko kuma wata hukuma da aka kafa sai ya tabbatar an rubutata a jaridar gwamnati wato gazttee kuma a buga dokar a jaridar Najeriya da ake iya karantawa a duk fadin kasar.

Amma wannan dokar har aka kaddamar da ita babu inda aka bugata aka sanarda da jama'a cewa ga abun da ake son a yi. Kamar yadda su nakasassu suka fada lokacin da za'a yi dokar yakamata an tuntubesu. Amma ba'a tuntubesu ba. Amsar da aka basu dangane da wasikar da suka rubutawa kakakin majalisar ta nuna cewa babu inda aka tuntubesu ko an buga kudirin yin dokar a wata jaridar kasar a tabbatar kowa ya gani kafin a tsayar da dokar. Wannan sabawa ne ga dokar gudanarwa ta majalisar.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Dokar Hana Barace-Barace A Jihar Kano - 2:28