An tattauna matsalar Boko Haram a taron kungiyar kasashen Afrika da ake gudanarwa a Afrika ta Kudu, inda Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci taron kwamitin tsaro da wanzar da zaman lafiya a Afirka.
WASHINGTON D.C —
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci taron kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU da ake yi a Afirka ta Kudu, sannan ya shugabanci taro kwamitin tsaro da zaman lafiya da aka yi jiya lahadi.
Inda aka tattauna matsalar rikicin Boko Haram da ya addabi Najeriya da makwabtanta irin su Kamaru da Chadi da Nijar, da kuma batun siyasa da yake ci ta farraka Sudan ta Kudu da ta Arewa.
Sakamakon wannan taron na kwamitin tsaron ya bayyana cewa, akalla sai matsalar Boko Haram ta lakume kudaden da za su kai kimanin dalar Amurka miliyan dari. Ga rahoton wakilinmu Muhammad Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5