Matsalar Almajiranci A Najeriya - laifin Wanene?

Duk da kokarin da wasu gwamnatoci da kungiyoyi ke yi game da maganar magance almajiranci a Najeriya wasu Malaman makarantun allo sun ce gwamnati ta baro shirin tun rani, game da maganar magance almajiranci a kasar.

Shugaban kungiyar malaman makarantun tsangaya a Najeriya reshen jahar Kaduna, Alaramma gwani Suleiman Idris Mai-zube, ya ce babu wani shiri kan Almajirai da zai yi nasara ba tare da shawarar malaman makarantun allo ba.

Kungiyar malam tsangaya ta fitar da tsarin inganta karatun allo da saka karatun zamani da kuma koya sana'o'i, amma gwamnati ba ta kula da tsarin ba, a cewar Alaramma Mai-zube.

Dr. Salisu Bala na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce an gaza wajen inganta tsarin karatun allo a Najeriya, inda ya nuna yadda wasu ke neman kudi da maganar Almajiranci a kasar.

Sai dai Hajiya Binta Kasimu wadda ke jagorancin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki da bankin duniya ta ce kungiyoyi ne kawai mafita kan almajiranci a Najeriya.

Hajiya Binta ta ce tuni bankin duniya ya gane hanyar amfani da kungiyoyi masu zaman kansu maimakon gwamnatocin Najeriya a matsayin mafita kan maganar barace-barace a kasar.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu Isah Lawal Ikara daga Kaduna:

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Almajiranci A Najeriya - Shin Ko laifin Waye?