Kimanin mayakan Boko Haram goma sha shida ne suka yi ajiye makaman su ga rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin tafkin Chadi.
Jami'in sadarwa na aikace-aikacen sojojin Najeriya, Kanar Aminu Ilyasu ya bayyana cewa wannan na zuwa ne bayan hare-haren da sojojin kasar suka yi ta kaiwa ba kakkautawa akan mayakan.
Mayakan na Boko Haram, wadanda suka ce baza su iya jurewa barin wutar dakarun ba, sun mika wuya ga sojojin hadin gwiwa wadanda su kuma suka mika su ga bataliya ta uku dake garin Gamborun Ngala.
Mayakan sun tabbatarwa sojojin ce wa da su aka yi ta kaiwa soji da fararen hula hari a baya, kafin su gaji da yakin.
Masana tsaro irinsu kanar Aminu Isa Kontagora na mai ra'ayin cewa yanzu kam tabbas dakarun Najeriya na samun nasara sosai.
Ga karin bayani a cikin sauti.
Facebook Forum