Ana zargin wata matashiya matar aure ‘yar kasar Japan da laifin yukurin kisan kai, alokacin da ta yanki mijinta da wuka a fuska. ‘yan sandan birnin Tokyo sunce wannan abu ya faru ne a dalilin wari da da mijin ta ya bari bayan da ya gama amfani da bandaki a gidan su.
matashiyar mai suna Emi Mamiya, yar shekaru 29, tace mijinta ya shiga bayan gida kuma yabar mata bandaki a turnuke da wari maras ‘dadi a ranar Lahadin data wuce.
Takuma ce mijin nata ‘dan shekaru 34 da haihuwa, ya shigar da ‘karamar ‘yar su mai shekaru 3 da haihuwa bandaki ba tare da ya fara wanke hannunsa ba.
Haushin wadannan abubuwane ne ya kai matar ga afkawa mijin ta da wuka har ta yanke shi a kumatun sa na hagu. jami’an ‘yan sandan Tokyo sun kama ta a gidan nasu, amma taki amincewa da laifin da ake tuhumarta da aikatawa.