Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Najeriya ta Din-Din-Dince Bata Wucin Gadiba


Siyasa a Najeriya
Siyasa a Najeriya

Siyasa a Najeriya tashiga wani sabon babi, inda aka taba samun nasara a karon farko da aka bama shugaba maici kaye, kuma a karon farko da jami’an hukumar zabe me zaman kanta wato INEC suka zama jami’ai nagari masu kishin kasa, don basu bari anyi amfani dasu ba.

Wato tarihi dai ya nuna cewar tun daga siyasar farko a Najeriya har zuwa zaben da aka gudanar kamin wannnan zaben shekarar, alkalumma nanuni dacewar kowane zabe na da nashi ‘yan korafe korafen, amma a karon farko wannan zaben na wannan shekarar yafita da ban. Inda shugaba kasa mai ci yayi ma zabbaben shugan kasar murna tunma kamin a bayyanar da sakamokon zaben, wanda a baya ya bama duniya tabbacin shi zai lashe zaben, amma sai ga akasin hakan.

Wannan dai ya nuna cewar demokaradiyya tazo don ta zauna kenan a Najeriya dama kasashen Afrika. Farfesa Kamilu Sani Fage na tsangayar ilimin siyasa a jami’a Bayaro, yayi fashin baki akan hakan, sanin kowane cewar idan akayi zabe wani zai ci kuma wani zai fadi, to mafi a’ala anan shine duk ‘yan takarkaru da magoya bayansu, su sani cewar babu yadda za’ayi ace kowa yaci, kuma idan wani bai aminta da sakamakon ba to kamata yayi abi ka’idoji wajen warware matsalolin cikin ruwan sanyi batare da wata matsalaba.

Wannan na nuni da cewar ‘yan siyasr Najeriya sun fara fahimtar ina duniya tasa gaba kenan, kuma yamata acigaba da wayarma al’uma kai dangane da hadduran dake tattare da banga ko hatsaniyar siyasa, wanda bai shafar manyan ‘yan siyasa sai talakawa, ashe yakamata al’uma suyi karatun ta natsu da harkar siyasa.

Malam. Nura Iro Ma’aji, daya dagacikin masu sa idon na kasa-da-kasa a lokacin zabe, yana ganin, abu mafi mahimanci a cikin shika-shikan zabe shine a samar da hukumar zabe me inganci, wada ba zatabi son kan gwamnati me ciba, to tahaka kawai za’aiya samun zabe me nagarta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG