Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taimakon Kai-da-Kaine Sana'ar Wankin Mota


Mota
Mota

Sana’a rigar ‘yanci! Babu wanda bai san wannan karin maganar ba, sai dai kawai asa son rai a zuci, kuma duk wanda ya tashi don nema to yana tare da nasara. Mafi akasarin matasa sun fison su kama sana’ar da zata kawo musu kudi cikin kankanin lokaci batare da wahalaba.

To me nene koma bayan hakan, Malam Nasiru Rabi’u, wanda ya kwashe shekaru yana sana’ar wankin mota, na ganin cewar kowace sana’a kasa a gaba kuma ka sa gaskia a cikin ta to lallai ba shakka zaka cinma nasara, ba dole sai ka fara daga sama ba kana iya farawa sannu a hankali ka kai inda kake bukatar kaiwa.

Kuma yayi nuni dacewar to kowane irin sana’a mutun zai iya samun alkhairi, wanda zai iya taimaka ma ‘yan’uwa da dangi, idan har yanada sha’awar hakan. Don haka babu wulakantattar sana’a idan ba mutun ya maida kanshi bayaba, don haka matasa mukama sana’a, wanda ta haka ne kawai zaka ga cewar ansamu al’uma me nagarta, tunda duk inda akace kowa ya ilmantu babu jahili to zakaga cewar babu wani wanda zai tada hankali ciki al’uma.

Idan akayi la’akari da kasashen da suka cigaba ai suma ba komai bane yasa suka zama abun da suke a yau ba, illa bama al’umarsu dammar ilmantuwa ne kawai ya kawo hakan, don haka yakamata gwamnatoci a kowane mataki su tashi tsaye wajen bama jama’a ilimi da samar da abubuwan more rayuwa da yake hakki na su, dan ta haka ne kawai al’uma bazasu sakansu cikin al’amuran da basu da amfani gare suba da kuma kasa baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG