Kasancewar asalin littafin da harshen larabci a ka rubuta shi, matashin malamin ya fassara shi zuwa harshen Turanci don amfanin akasarin ‘yan boko da ke karatu a Islamiyya da kuma kaunar nazari a litattafa daga gida.
Shugaban tsangayar shari’ar Musulunci na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, Farfesa Muhammad Bello Uthman ne dai ya yi bitar fassarar, ya ba da shawarar a dau littafin a sanya a manhajar makarantu don dalibai su amfana da shiriyar da ke ciki.
Farfesa Muhammad Bello ya yi amfani da dabarar musamman ga yara kanana zai sa al’ummar da ke tasowa nan gaba ta zama mai gaskiya da amana.
Marubuci kuma mahaddacin Alkur’ani Abubakar Musa ya ce burin sa shi ne in ya na tafiya musamman a jihohin arewa ya ga dukkan matasa na karatu da fahimtar abun da su ke karantawa.
Musa ya ce Najeriya na bukatar malamai masu koyarwa cikin hikima ne don cusa akida mai kyau ga sauran jama’a.
Daya daga mata a wajen taron Hajiya Kaka Kumaliya ta bukaci maza su rika taimaka wa mata wajen tarbiyyar yara.
Taron, wanda ya gudana a cibiyar bunkasa rayuwar mata da matasa a Abuja, ya samu halartar dandazon dalibai da su ka haddace Alkur’ani da kuma wasu mutane da su ka ba da gudunmowa don cigaba da samar da kofen littafin.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5