Taron kaddamarwar ya gudana a Masallacin Ansaruddeen da ke anguwar Wuse 2 a Abuja.
Bayan idar da sallar Jumma’a an jera kofin fassarar inda malamai su ka yi bayanin muhimmancin irin wannan aiki don samar da ilmin Alkur’ani ga jama’ar da ke amfani da harsunan su na asali don fahimtar ma’anonin cikin sauki.
“Na shafe shekaru 5 ina gudanar da wannan aiki kafin na kammala, kuma mun tura kofi 50 kasar Igbo inda mutum 24 su ka karbi Islama.” In ji Sheikh Ohajimadu.
Shehun malamin ya kara da cewa akwai fassarar Alkur’ani a harshen Hausa na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da wani da a ka yi a harshen yarbanci, wanda hakan ya ba shi kwarin gwiwar gudanar da aikin fassarar don al’ummar Igbo su amfana.
Alhaji Shahru Umar ne ya jagoranci taron kaddamarwar ya na mai cewa aiki ne mai muhummanci da su ka sanyawa hannu don samun kammala shi.
Hakimin Galadimawa a Abuja Alhaji Musa Barde ya bukaci sauran masu hannu da shuni su tallafa don samar da kofin fassarar mai yawa don a cigaba da rabawa jama’a.
Mutane sun yi dafifi su na bude kofin su na dubawa duk da akasrin su ba sa fahimtar harshen Igbo in ka debe NSO da a ka ce na nufin mai tsarki wato NSO ALKUR’AN, Sai CHUKWU-Allah mai girma.
Saurari cikakken rahoton a sauti: