Matashin Da Ya Taka Daga Legas Zuwa Arewa

Wani matashin da ya sha alwashin takawa da kafa daga birnin Legas zuwa Abuja ya isa garin Bidda na jihar Naija.

Malam Suleman Hashimu wani matashi ne wanda ya sha alwashin yin tattaki daga daga duk inda yake a fadin Najeriya, zuwa birnin Abuja da zarar Janar Muihammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya gabata.

Rahotanni na cewa, matashin ya fara tafiyar ne daga jihar Legas kuma a halin yanzu matashin wanda makonsa na biyu kenan da fara tafiyar ya kai jahar Naija kuma ya sami gagarumar tarba daga shugaban majalisar sarakunan jahar Naija, Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar a fadar sa dake Bidda.

Malam Suleman ya yi karin bayanin cewa da farko ya dan sami shakka sabo da wasu dalilai amma ganin yadda mutane ke nuna masa kauna sai ya mike.

A hirar sa da wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, ya yi bayanin cewar ya ya fuskanci wasu ‘yan kalubale amma hakan ba zai taba sa shinya daina ba.

A halin yanzu dai matshin na cigaba da tafiyar sa kuma a cewar sa, ba lallai sai ya yi ido hudu da zababben shugaban ba.

Babban burin shi kawai ya cika alkawarin sa na isa birnin Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Matashin Da Ya Taka Daga Legas Zuwa Arewa - 2'01"