Matasan kirista da musulmai na kabilar jukun sun kafa turban zaman lafiya

Matasa

Jihar Taraba ta jima tana fama da rikicin addini da na kabilanci dalili ke nan matasan kirista da musulmai na kabilar Jukun inda rikicin ya fi kamarari suka tattauna tsakaninsu da zummar kafa turban zaman lafiya

Kungiyar wanzar da zaman Lafiya ta kasa da kasa ta yabawa yukurin matasa mabiya addini Kirista da Musulumci yan kabilar Jukun na karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba da kafa turban zaman maido da zaman Lafiya da fahimtar juna a yankin da rikicin addini ya dabaibaye.

Sakatariyar kungiyar Madam Charity Kande Garba ce ta furta haka lokacin da ta ke marhaban da yukurin da matasa mabiya addinan biyu suka yi na kawo karshe tashe-tashen hankula sakanin Kiristoci da Musulmai tana cewa kungiyar zata taimaka da shawarwari domin dorewar shirin.

Shugabannin kungiyoyin biyu Mal. Abdullahi Maikasuwa da Mr, Zando Haku sun ce muradan hadin kansu sune kauda da kyama, kyautata zaman Lafiya, da fahimtar juna tsakanin al'umominsu. Suna masu cewa nan gaba ba zasu kyale wasu tsirarru su rika anfani da matasa domin ruruta rikicin addini a yankin.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan kirista da musulmai na kabilar jukun sun kafa turban zaman lafiya - 3' 12"