Lura da muhimmancin gudummuwar da matasa ke bayarwa wajen yada manufofin jam’iyyun siyasa a fagen siyasar jamhuriyar Nijer ya sa kungiyar AEC shirya taron horo ga wasu gomman matasa don ganar da su hanyoyin kaucewa fadawa tarkon ‘yan siyasar da ke ci da gumin magoya bayansu kamar yadda mamba a kungiyar ta Alternative Kaka Touda Goni ya bayyana wa muryar Amurka.
Mu’amulla ta tsakanin matasa da shugabanin jam’iyyu, da batun ‘yancin matasa a jam’iyyun siyasa da hakkin da ya rataya a wuyansu a jam’iyance na daga cikin abubuwan da aka tanttauna akansu a ranakun farkon wannan zama.
Samun masaniya akan yanayin tafiyar siyasar duniya a yau da huldar kasa da kasa abu ne da ya zama wajibi ga dukkan wani mai fatan jagorancin jama’a a wannan zamani, a saboda haka aka saka wannan maudu’i a jerin abubuwan da za a baje akan teburin wannan haduwa.
Wayar da kan matasa a game da tafiyar sha’anin siyasa wani abu ne da jam’iyyun siyasa ka iya yi wa wata karkataciyar fassara, mafari kenan kungiyar da ta shirya wanann haduwa ta kare kanta daga dukkan wani zargi.
An dai bayyana cewa bayan wannan taro na tsawon makwanni 2, mahalartansa za su yada abubuwan da suka koya domin sauran takwarorinsu matasa a jam’iyyu dabam daban ta yadda za a kara samun wayayyun matasan da suka lakanci takun da zai kare su daga bangar siyasa ko turin motar siyasa da dai sauran dabi’un da ke dabaibaye ci gaban matasa a kasar da kashi 70 cikin 100 na al’umarta matasan ne.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5