Matasan Fulani Kan Mahimmancin Zaman Lafiya

Fulani makiyaya

Kungiyar matasan Fulani ta yi taron fadakar da kawinan mutane kan mahimmancin zaman lafiya
Kungiyar matasan Fulani da ake kira Fuldan ta yi taron fadakar da kawunan matasa Fulani mahimmancin zaman lafiya tsakaninsu da sauran al'umma.

Taron ya yi nazarin halin da Fulani matasa suke fuskanta da suka hada da rashin aikin yi da kuma karancin samun guraben cigaba da karatunsu bayan sun kammala makarantar sakandare.

Malam Kabiru Musa, shugaban kungiyar a jihar Bauchi ya yi bayyani kan makasudin taron. Ya ce sun yi taron ne domin su fadakar da matasan Fulani su kuma tattauna abubuwan dake ci masu tuwo a kwarya dangane da cigaba. Ya ce su a jeji suke kuma basa neman tashin hankali. Suna kawar da kansu daga duk abun da ka iya kawo rikici tsakaninsu da manoma sabo da su zauna lafiya. Ya ce suna yin biyayya da kungiyoyin iyayensu a matatsayinsu na matasa.

Sakataren kungiyar Ibrahim Makau ya yi karin haske kan al'amuran da suka shafi rashin aikin yi da kuma ilimi. Ya ce sun zo ne su yi taron su tattauna kan abubuwan da suka kamakata a yi masu da kuma yadda aka barsu a baya. Misali akwai wadanda suka gama makarantu suna neman aikin yi basu samu ba. Kungiyarsu tana kokarin samo masu aiki. Wadanda kuma suka gama karatun sakandare amma suna son su cigaba suna kokarin samar masu shiga makarantun da suke so.

Malam Sha'aibu Abubakar dattijon kungiyar ne ya yi bayani kan rikicin Fulani da manoma da kuma hanyar da za'a bi a warware matsalar. Kungiyar dai ta kudiri aniyar kewayawa duk fadin Najeriya domin wayar da kawunan Fulani a samu zaman lafiya.

Abdulwahab Muhammed nada cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Fulani Kan Mahimmancin Zaman Lafiya - 3:37