A yayin da wasu ke shirin shiga zanga-zangar juyin juya hali a Najeriya, hadakar kungiyoyin matasan Arewacin Nigeriya mai suna Coalition of Northern Groups ta ce kada wani dan Arewa ya shiga zanga-zangar don akwai lauje cikin nadi.
WASHINGTON DC —
Shugaban kungiyar Alh. Nastura Ashir Sharif wanda ke amsa tambayoyi a wajen taron manema labarai a garin Kaduna yace zanga-zangar ba ita ce mafita ba. Yace komawa kan teburin tattaunawa itace zata kawowa kasar zaman lafiya fiye da zanga zanga.
Saidai kuma shugaban hadakar kungiyoyin arewachin Najeriyan Ashir Sharif ya ce wajibi ne shugaban kasa Buhari ya yi kyara a tsarin tafi da gwamnatin shi.
Shirin shiga zanga-zangar na wannan ranar litinin dai ya jawo cecekuce tsanin 'yan daga bangarori daban-daban saboda ganin gwamnatin ta shugaba Buhari ba ta ma gama zama don cin wa'adin ta na biyu ba.