Rundunan ‘yan sanda a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta baza jami'anta don gano wadanda suka kashe wani fitaccen dan sa-kai na kungiyar Miyetti Allah, da ke taimakawa wajen kamo bata gari, Alh. Saidu Sale Kolaku.
Kolaku shi ne mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah mai kula da yankin Adamawa ta kudu da ya kunshi kananan hukumomi bakwai.
An kashe shi ne a gidansa da ke garin Mayo-Belwa, wannan kuma na zuwa ne bayan da rundunan 'yan sandan jihar ta karrama shi kasa makonni biyu da suka gabata, akan irin rawar da yake takawa wajen kamo masu garkuwa da jama'a.
Jami'in hulda da jama'a na kungiyar Miyetti Allah a jihar, Muhammad Jika Buba ya tabbatar da aukuwan lamarin.
Ya kuma ce, ba za su ja baya ba wajen taimakawa jami'an tsaro, suna nan daram.
Kawo yanzu rundunan ‘yan sandan jihar ta bakin kakakinta, DSP Suleiman Yahya Nguroje, ta ce za ta bi diddigin wannan kisan gilla, tana mai mika ta'aziyyarta ga iyalan mamacin.
Facebook Forum