Irin hakan ya faru a jihar Sakkwato dake arewacin kasar inda matasa suka husata suka kona ofishin ‘yan sanda da wani da ake tuhumar dan bindiga ne, saboda an hana su daukar doka a hannun su.
Da safiyar ranar talata ne wasu da ake tuhumar ‘yan bindiga ne suka shiga wani kauye mai suna Kainuwa su ka yi fashi gidan wani Alhaji, inda bayan sun wuce jama'ar garin suka bi sawun su, suka tarar da wasu mutane 6 suka kama su akan tuhumar su ne barayin.
Daga nan suka hannun ta su ga jami'an ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.
Rundunar 'yan sanda ta jihar ta bakin kakakin ta ASP Sanusi Abubakar tace bayan da DPO ya karbi mutanen sai jama'ar suka nuna bukatar a basu su su kashe.
Karin bayani akan: ASP, Sanusi Abubakar, ‘yan bindiga, jihar Sakkwato, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Wannan na zuwa ne lokacin da wasu al'ummomi ke ta fuskantar hare-haren ‘yan ta'adda musamman a gabascin Sakkwato duk da watan azumi da ake ciki.
Bisa ga yadda jama'a ke kokawa akan ayukkan ta'addanci da ke salwantar da rayukan da dukiyoyi, rashin samar da hanyoyin magance wannan matsalar kan iya haifar da wasu matsaloli a nan gaba kamar yadda alamu suka nuna na jama'a na son a bari su kashe yan ta'adda da kan su.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5