Yayin da mabiya addinin kirista a fadin duniya ke cigaba da bukukuwan kirsitimeti dana sabuwar shekara, matsalar da ta fi daukar hankali a Najeriya ita ce ta karancin man fetur da kuma rashin samun albashi a wasu jihohin kasar.
To sai dai kuma duk da wannan matsalar, a bana an gudanar da bikin kirsimetin cikin kwanciyar hankali ba kamar shekarun da suka gabata ba, musamman a jihohin da rikicin Boko Haram ya fi shafa na Adamawa, Borno da kuma jihar Yobe.
Wasu yara a Yola, da Jalingo fadar jihar Taraba, sun nuna farin cikinsu da bikin na bana, inda suka ce sun ci nama da abubuwan tande-tande. Haka kuma su ma matasa sun ce bana Allah San barka. Fata dai shine Allah Sa a kammala bukuwan cikin lafiya, yayin da jami’an tsaro ke cigaba da shawagi cikin shirin ko ta kwana.
Domin karin bayani, saurarai rahoton Ibrhaim Abdul'aziz a nan.
Your browser doesn’t support HTML5