Matasa Kan Kirkiro Sabon Salon Magana Dai Dai Da Zamani

Kamar yadda kowane harshe ko kabila ke samun wasu sababbin kalmomi da ke tafiya da zamani, wasu kalmomi kuma ke neman bacewa sakamakon rashin amfani da su, haka matasa a wurare daban daban ke kirkiro wasu bakin kalmomi ko salon mgana domin zantawa da juna ba tare da wasu baki sun fahimci sakon da suke aikawa juna a lokacin ba.

Ta dalilin haka ne muka sami zantawa da wani matashi mai suna Ibrahim Abdullahi, wanda ya bayyana cewa a duk lokacin da kaji matasa a yankinsu sun ambaci “kidan janaral a sama” suna nufin gari yayi zafi Kenan.

Ya take a yankinku, wane salon Magana matasa ke amfani da ita data yi dai dai da zmani?

Saurari wasu bakin kalamai adaga Ibrahim Abdullahi a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Ibrahim Abdullahi: Matasa Kan Kirkiro Sabon Salon Magana Dai Dai Da Zamani