Jarumar fina finan Hausa Kannywood Rahama Ibrahim Sadau, ta ce, filin saukar jiragen sama na jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ya fi kowane filin jirgi rashin ingantattun ayyuka a duk fadin kasar
Rahama Ibrahim Sadau, ta bayyana daukacin ma’aikatan filin jirgin saman jihar ta kaduna a matsayin marasa mutumta jama’a.
A shafinta na twitter, me adireshi @Rahama_sadau, ta rubuta cewar “babu filin jirgin sama da na taba gani mai rashin ayyuka masu nagari kamar na jihar Kaduna. Dukan ma’aikatan basu ganin mutumcin mutane tamkar kai ka rike masu albashi ko kuma ka tilasta masu zuwa aiki da asuba”
Ta kuma kara da cewa “kai dai bari ni naga abinda na gani, tamkar dukansu basu da halin kirki.”
A kwanankin baya ne jarumar ta fuskanci hukuncin korarta daga Kannywood, wanda hukumomin kula da harkokin fina finan Hausa MOPPAN suka yi sakamakon runguma da hada jiki da jarumar ta yi da namiji a wani bidiyon wakar soyayya.