Matan Sojojin Nijar Sun Bukaci Tallafi Daga Gwamnatin Kasar

Matan sojoji a wuraren da ke fama da matsalar tsaro a jamhuriyar Nijar sun bukaci hukumomi da su tallafa masu da jarin gudanar da kananan sana'o’in da za su ba su damar daukar dawainiyar bukatun yara musamman a tsawon lokutan da mazajensu su ka yi tafiya mai nisa don aikin sintiri.

Wadannan mata wadanda ke magana a karkashin inuwar kungiyar matan sojoji a yankin Diffa mai fama da matsalar Boko Haram sun fara ne da yaba wa hukumomi akan abinda suka kira dagewa game da maganar tabbatar da tsaron kasa, daga nan kuma suka bukaci a tallafa masu da jari.

Shekaru sama da 4 kenan da yankin Diffa da ke Kudu maso Gabashin Nijar ke fama da matsalar Boko Haram lamarin da ya haddasa asarar dimbin fararen hula da jami’an tsaro.

Shugaban kasar Nijar a yayin ziyarar da ya kai a wannan yanki a karshen makon jiya ya yaba da nasarorin da askarawan kasarsa ke samu a yakin da suke gobzawa da ‘yan ta’addan BH sannan ya ce ya gamsu da yadda al’ummar yankin Diffa ta yi tawakalli akan halin da ta tsinci kanta ciki sakamakon lura da yadda kowanensu ke kare mutunci kansa ta hanyar neman halaliya.

Saurari rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Matan Sojojin Nijar Sun Bukaci Tallafi Daga Gwamnatin Kasar