Abubakar Alhassan babban jami'i a Hukumar KMA ya fadawa Muryar Amurka cewa hukumar ta dau wannan mataki ne sakamakon wasu rahotanni da wasu asibitoci tare da yan sanda suka bayar game da gudunmuwar da yan adedeta ke bayarwa wajen hatsura tare da wasu miyagun ayyuka; "rashin tsaranta aikin yan adedeta ya sanya hukumar daukan wannan mataki saboda rahotannin da asibitoci da hukumar 'yan sandan yankin Ashanti suka fitar ya nuna cewa hatsuran da ake samu yawancinsu sakacin 'yan adedeta ke haifarwa. Mun yi zama a matsayin mu na kwamitin tsaro da adalci a hukumar KMA kuma zamu inganta wannan dokar da zata hana adedeta sahu shiga wasu unguwanni cikin Kumasi. Duk wadda ya keta wannan doka to za'a ladabtar da shi"
Wani direban adedeta mai suna Asbat Sidi Ali da ya kammala jami'a tun shaikarar 2015 ba tare da samun sana'ar yi ba ya yi fargaba bisa makomarsa da iyalinsa muddan wannan doka ta tabbata; "da na kammala jami'a, ban samu sana'ar yi ba sai nayi kokari na samu adedeta na saya ina aiki da shi ina ciyar da iyali na. Cikin wannan sana'a muke rayuwa kadan kadan. In kuwa wannan mataki ya tabbata, gaskiya zai kawo mana damuwa sosai"
Shi kuwa Yushau Abdul Mumin mai sharhi kan alamurran yau da kullum ya bayyana cewa, "wannan mataki kuwa in aka dauka , dubban yan adedeta ne za su rasa sana'ar yi.
"A cikin garin Kumasi yawan adedeta ya kai dubu ashirin da takwas zuwa talatin. Masu mallakan adedeta da direbobinsu ne ke cin abinci ta wannan sana'a. Kuma wasu da suka shigo cirani a Ghana kamar Hausawa Nijar da Najeriya da Burkina Faso duk suna sana'ar adaidaita . Don haka wannan mataki zai kawo matsala babba" inji shi.
Hashim Iddi Madani shugaban hukumar da ke wayar da kan jama'a domin kiyaye hatsura ayankin Ashanti NRSF, ya ce sakaicin shugabannin adedeta ne ya haifar da wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka; "shugabannin yan adedeta sun yi sakaici abin da ya sanya hukumar shirin daukan wannan mataki kenan."
Shugaban yan adedeta a Kumasi Nurudeen Muhammad ya ce sun fara shirye shiryen tsaftace sana'ar tasu ta hanya ganawa da masu ruwa da tsaki ciki har da gwamnati domin ganin ba dauki wannan mataki akansu ba.
Tun shekarar 2015 da wannan sana'a ta kafu a Kumasi dubban matasa ne suka samu abin yi amma kuwa rashin tsaftace wannan sana'ar ka iya sanya dubban matasan Ghana da ma wasu yan kasashen ketare asaran sana'ar yi.
Saurari rahoton Hamza Adam a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5