Harkoki sun tsaya cik sakamakon wani yajin aikin gargadin da ‘ya’yan kungiya ta ‘yan keke-napep, wato ‘yan acaba suka faro a jihar Adamawa, dominn nuna fushin su game da wata sabuwar doka ta amfani da lasisin tuki wanda hukumar kiyaye hadura a Najeriya, Federal Road Safety Commission (FRSC), ta kaddamar a kan kudi Naira dubu hudu da dari daya.
Wasu mutanen da wannan yajin aikin ya shafa sun bayyana matukar damuwarsu sun kuma ce lamarin ya shafi tattalin arziki da harkokin yau da kullum. Wasu a cikin sun ce ‘ya’yansu basu je makaranta ba saboda rashin abin hawa, wasu yaran makaranta kuma sun yui tafiya mai nisan gaske kafin suka isa makaranta.
Direbobin na adaidaita Sahu na Keke Napep, sun koka da wannan doka. Abubakar Aliyu da Abubkar Hassan na cikin matuka keke napep sun bayyana rashin jin dadin su a kan yanda gwamnati take kokarin aiwatar da wannan sabuwar doka cikin geren lokaci, lamarin da ka iya jefasu cikin damuwa.
Shiko Kwamared Bashir Muhammad Jimeta na cikin shugabanin kungiyar masu keke Napep a jihar Adamawa, yace koda yake wannan yajin aiki ba da yawunsu aka shiga ba, to amma akwai abin dubawa.
Mako biyu da suka wuce ne Hukumar Kare Hatsira ta kasa ta FRSC, ta sanar da fara yin katin Lasisin tuki ga ‘yan acaba da cewa dokar zata fara aiki a ranar daya ga watan Agustan gobe. Idris I. Fika babban jami’in hukumar ne mai kula da aiki da cikawa a jihar Adamawa, ya bayyana manufar dokar.
Abin Jira agani shine ko yaya lamura zasu kasance sakamamon wannan yajin aiki.
Ibrahim Abdulaziz yana dauke da karin bayani:
Facebook Forum