Niamey, Niger - A sanarwar da ta bayar, gwamnatin mulkin sojan Mali, ta zargi kasashe mambobin kungiyar ta G5 Sahel da nuna rashin adalci a bisa la’akari da yadda ta ce sun hana ta shugabanci a tsarin karba-karbar kungiyar, a wani lokaci da kamun ludayi ya zo gare ta. A cewar tsohon ministan tsaron kasar Nijer Kalla Moutari wannan mataki ragaggar dabara ce.
Yaki da ta’addanci a yankin Sahel na daga cikin ayyukan da kungiyar ke maida hankali akansu ta hanyar rundunar hadin gwiwar kasashe 5 mambobin G5 Sahel, abinda ya sa ake ganin ficewar Mali na iya maida hannun agogo baya.
Sabon matsayin da hukumomin Mali suka dauka tun bayan tagwayen juyin mulkin da aka fuskanta a kasar a wani lokaci da har yanzu ake cikin halin rashin tabbas game da shirya zaben dimokradiyya, shi ne abin da ake dauka a matsayin dalilan da ya sa kasashen G5 Sahel suka hana wa Mali dare kujerar shugabancin kungiyar, inji mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum.
A shekarar 2014 ne kasashen Nijer Chadi Burkina Faso Mauritania da Mali suka kafa kungiyar G5 Sahel da zummar karfafa hulda a tsakaninsu. Tabarbarewar tsaro a wannan yanki ta sa shugabannin wadannan kasashe kafa rundunar hadin gwiwar G5 Sahel a 2017 da nufin yaki da kungiyoyin ta’addanci, sai dai mutuwar shugaba Idriss na Chadi da juyin mulkin da aka fuskanta a kasashen Mali da Burkina Faso sun yi sanadin durkushewar harkokin wannan runduna, lamarin da hatta sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwa akan faruwarsa, kamar yadda ya sanar a yayin ziyarar da ya kawo a baya bayan nan a Nijer.
Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma:
Your browser doesn’t support HTML5