Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Taron Zaman Lafiyar Jihar Tilabery Ya Damka Wa Shugaban Kasa Rahoton Ayyukansa


Taro
Taro

Kwamitin da ya jagoranci babban taron zaman lafiya da hadin kan al’umomin jihar Tilabery ya damka rahoton karshen wannan taro ga shugaban kasa Mohamed Bazoum domin sanar da shi mahimman shawarwarin da aka tsayar.

Wannan na zuwa ne a yayin wata haduwa ta neman bakin zaren warware matsalolin tsaron da ake fama da su shekaru kusan 10.

Sai dai kungiyar makiyayan arewacin jihar ta yi korafi akan abinda ta kira wariyar da aka nuna a yayin shirya wannan zama.

Taron wanda ya hada illahirin shugabanin rukunonin al’umar jihar Tilabery da hukumomi a karshen watan maris din da ya gabata ya kasance wani lokaci na binciko dalilan da suka hadassa lalacewar al’amuran tsaro a jihar mai makwaftka da kasashen Mali da Burkina faso inda kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan bindiga ke cin karensu ba babbaka.

Wata 1 bayan haka kwamitin da ya tsara wannan zama ya gabatar da rahoton ayyukansa ga shugaban kasa don sanar da shi abubuwan da ya gano.

Tsohon ministan raya al’adu Assoumana Malan Issa na daga cikin shika shikan wannan taro. Yace hare-haren da ake ta kaiwa cikin Tilaberry, rigingimu ne da su ka hada da na kabilanci.

Domin warware wannan kulli kwamitin na ‘yan jihar Tilabery ya zo da wasu shawarwarin da ya ke dauka a matsayin hanyoyin samun mafita.

To sai dai shugaban kungiyar makiyayan arewacin jihar Tilabery Boubacar Diallo na cewa akwai alamar an yi kitso da kwarkwata.

Shugabanin kwamitin da ya tsara wannan taro na Forum de la Paix et de la cohesion sociale sun bukaci hukumomi su yi afuwa ga wani shehun malami dan asalin jihar Tilabery da alkali mai zargi ya kulle a kurkuku yau watanni sama da 2 saboda zarginsa da yi wa Nijer muguwar addu’a lokacin da ya halarci wani gangamin ‘yan asalin jihar tilabery da ya gudana a Yamai.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG