An bayyana rabon kudaden shigar ne a yayin taron kwamitin rabon arzikin kasa (FAAC) na watan Oktoba, da ya gudana a Abuja.
A cewar sanarwar da jami’in yada labaran ofishin babban akanta na tarayya, Bawa Mokwa, ya fitar, jumlar Naira tiriliyan 1. 298 ta kudin shigar da aka raba sun hada da naira biliyan 124.716 da aka samu daga harajin da aka karba daga hannun mutane da hada-hadar kasuwanci da Naira biliyan 543.518 ta harajin sayen kaya (VAT) da naira biliyan 18.445 ta harajin aikewa da kudi ta na’ura da naira biliyan 462.191 ta harajin musayar kudade da naira biliyan 150, 000 ta ribar data doru a kan ajiyar jumlar kudaden shigar.
Sanarwar bayan taron da kwamitin rabon arzikin kasar ya fitar ta nuna cewa jumlar kudaden shigar da aka samu a watan Satumbar 2024 ta kai naira tiriliyan 2.258.
An zaftare jumlar naira biliyan 80.993 a matsayin ladan tara harajin a yayin da aka yanke naira biliyan 878.946 a matsayin ladan aikewa da kudaden shigar da tallafi har ma dana biyan bashi.