Matakan Da Hukumomin Nijar Suka Dauka Don Dakile Yaduwar Cutar Murar Tsuntsaye

Ma'aikatan kiwon lafiya a Hong Kong suke yanka kaji da ake zaton sun kamu da murar tsuntsaye.

Daga cikin matakan har da hana shigowa da tsuntsaye daga tarayyar Najeriya, inda a ke ganin daga nan ne cutar ta bullo.

BIRNIN N’KONNI, NIGER -Biyo bayan bullar cutar murar tsuntsaye a cikin Jihar Taahoua, musaman a gundumar Buza da ke gabas maso Arewacin birnin N'Konni, da babban birnin Yamai, hukumomin kiwon lafiyar dabbobi da ke kan iyakar Nijar da Najeriya sun fara daukan wasu matakai,.

Daga cikin matakan har da hana shigowa da tsuntsaye daga tarrayar Najeriya, inda a ke ganin daga nan ne abin ya bullo.

Ma'aikatan kiwon lafiya a Hong Kong suke yanka kaji da ake zaton sun kamu da murar tsuntsaye.

Shugaban ma'aikatar kiwon lafiyar dabbobi na birnin N'Konni, Dakta Issaka Alio Farka da ke kilomita biyu da iyaka da Najeriya, ya ce a kowace safiyar Allah, dumbin matasa ne daga Jamhuriyar Nijar ke kutsawa a sako da lunguna na birane da Kauyukan arewacin tarrayar Najeriya domin neman kaji ko zabi ko tantabaru da talo-talo.

Ya kara da cewa, sukan cika motoci masu tarin yawa da tsuntsayen domin kai su birnin Yamai inda farashin ke haurawa a kowace rana.

Matasan da ke wannan sana'ar da ma safarar tsuntsayen zuwa babban birnin na Yamai domin sun ce akwai irin matakan da suke dauka na kiyaye kawunansu, al'umma da ma kasar ta Jamhuriyar Nijar, domin dakile yaduwar cutar ta murar tsuntsaye.

CUTAR MURAR KAJI

Hukumomin kiwon lafiyar dabbobi na wannan kasar, suna da tanadi na ko ta kwana game da irin wannan matsalar, kuma tuni suka motsa matakan hana shigowar tsuntsaye da ke dauke da wannan cutar a cikin kasar in ji Dakta Issaka Alio Farka.

Daga dai cikin gargadin da hukumomin kiwon lafiya ta wannan kasar ke ci gaba da wallafawa, har da tabbatar da dafa naman tsuntsaye har ya yi murus kafin aci.

Saurari cikakken rahoto daga Haruna Mamane Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Matakan Da Hukumomin Nijar Suka Dauka Don Dakile Yaduwar Cutar Murar Tsuntsaye