Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfana Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Aisha Ahmed, Mataimakiyar Gwamnan CBN

Aisha Ahmed, Mataimakiyar Gwamnan CBN

Mataimakiyar Gwamna a Babban Bankin Najeriya CBN, Aisha Ahmed ta ce sun yi odar sabbin kudin da aka sauya fasalinsu har na Naira miliyan dari biyar, amma ta gagara fadin ko nawa aka kashe wajen buga su.

ABUJA, NIGERIA - Aisha ta gurfana a gaban Majalisar Wakilan Najeriya ne a madadin Gwamnan na Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele wanda aka ce yana can kasar waje yana duba lafiyarsa.

Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfana Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfana Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Idan ba a manta ba, Majalisar wakilai ta sauya zamanta a lokuta daban daban har sau uku domin a samu Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan sauya fasalin kudi da ya yi ba tare da tuntubar Majalisar ba. A karshe dai jiya Alhamis ne mataimakiyar Gwamna mai kula da harkokin kudi, Aisha Ahmed ta wakilce shi.

A lokacin da Aisha Ahmed ta ke amsa tambaya kan ko nawa ne CBN ta kashe wajen yin odar sabbin kudaden da aka sauya wato Naira 1000 da Naira 500 da kuma Naira 200, sai ta ce ta san an yi odar sabbin kudin har na Naira miliyan 500 amma ba ta san nawa aka kashe wajen buga su ba.

Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfana Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfana Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Yawancin ‘yan Majalisan ba su gamsu da bayanan Mataimakiyar Gwamnan ba ciki har da Mohammed Gudaji Kazaure, inda ya ce ba a ba shi dama ya yi mata tambayoyi ba, amma inda ya samu dama zai tambaye ta dalilan da suka sa CBN bai bude asusun zuba kudaden Stamp Duty ba.

Gudaji ya ce inda an bude wadannan asusun zai yi amfani da kudaden wajen biyan basukan da kasar ke ci, sannan a yi ayyukan ci gaban kasa da su. Gudaji ya koka da yadda wannan tsari na rage mu'amala da tsabar kudi zai kuntata wa ‘yan kasuwa, musamman ma wadanda ke karkara.

Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfana Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Shi ma Gagarabadan Majalisar, Mohammed Tahir Monguno, ya koka ne akan lokacin da aka dibar wa sauyin kudin inda ya ce a Jihohi irin su Borno da Yobe akwai kauyuka da dama da ba su da bankuna sai sun je shelkwatar Karamar hukuma, kuma haka ba shi da sauki a gare su.

Monguno ya ce idan Majalisa ta dawo hutu zai tada maganar saboda a tattauna sannan a samo mafita.

An fara kaddamar da tsarin nan na rashin mu'amala da tsabar kudi da ake kira CASHLESS POLICY a turanci a shekarar 2012, kuma an kaddamar da shi ne a karkashin sashi na 2 da na 47 na dokar da ta kafa Babban Bankin Najeriya CBN.

Saurari cikakken rahoton daga Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakiyar Gwamnan CBN Aisha Ahmed Ta Gurfanar Gaban Majalisar Wakilan Najeriya.mp3