Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Kudin Naira


Sabbin takardar kudin Naira
Sabbin takardar kudin Naira

Ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira, inda ya bayyana farin cikinsa kan yadda hukumar buga kudin kasar ta (NSPM) ta sake fasalin kudaden.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da sabbin takardun kudin da aka yi gabanin wani taron majalisar zartarwar tarayya, shugaban ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ya amince wa babban bankin Najeriya (CBN) kan ya sake fasalin takardun kudin Naira 200, 500, da kuma 1000.

A cewar Shugaban, an sanya wa sabbin takardun kudin wata fasaha ta yadda zai yi wuya wasu su buga jabunsu.

Ya kuma kara da cewa sabbin kudin za su taimaka wa babban bankin kasar tsara da kuma aiwatar da manufofin kudi mafi kyau.

Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnan babban bankin CBN Godwin Emefiele da mataimakansa bisa wannan shiri, yayin da ya kuma gode wa babban daraktan bankin, da sauran shugabanni, da ma’aikatan hukumar buga kudi na Najeriya saboda aikin da suka yi tukuru da babban bankin don ganin sake fasalin kudin ya tabbata, da kuma yadda suka buga sabbin kudin cikin dan kankanin lokaci.

Da yake bayani game da bukatar manyan bankunan kasa da hukumomin kasa su fitar da sabbin kudi ko sake fasalin takardar kudin kasa a cikin shekara 5 zuwa 8, shugaban ya ce yanzu kusan shekara 20 ke nan tun bayan da aka sake fasalin kudin kasar.

Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

“Ana sake fasalin takardar kudi ne da nufin cimma wasu manufofi, ciki har da inganta takardar kudin, rage yawan jabun kudi, sa ido kan kudaden da ake amfani da su a kasa, rage kudin da ake kashewa wajen kula da kudi,” a cewar shugaba Buhari.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG