Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Yayi Zaman Sulhu da 'Yan Jam'iyyarsu ta PDP

Namadi Sambo.

Yayin da wasu 'yan jam'iyyar PDP ke ta yin korafi game da yadda aka fitar da 'yan takarar zaben 2015, mataimkin shugaban kasa ya nemi yin sulhu.

A taron da suka yi a Kaduna, Namadi Sambo mataimakin shugaban kasa ya yiwa 'yan jam'iyyar jihar Yobe alwashin tafiya tare.

Yace gwamnati ba zata bar kowane dan jam'iyyar a baya ba. Yace daya daga cikin abun da suka tattauna shi ne idan suka kafa gwamnati za'a tafi da kowa da kowa. A gwamnatin tarayya duk wanda yayi takara ba za'a barshi ba. Kowa zai samu abun da zai dafa a cikin gwamnati.

Alhaji Adamu Maina Waziri dan takarar gwamna a jihar Yobe yana kan gaba wurin sulhunta 'yan PDP din daga jihar Yobe. Yace sun duba abun da ya faru baya tsakaninshi da Dr. Yarima Ngawa kuma an yafi juna kuma sun amince su yi abu daya tare, wato su hada kai su samu nasara domin su ceto al'ummarsu daga cikin ukubar da gwamnatin jihar ta yanzu ta jefasu.

Dr Adamu Bulama dake cikin gwamnatin tarayya daga Yoben yace sun yi shekara goma sha shida karkashin gwamnatin APC a jihar. Babu abun da suka samu sai zalunci da danniya.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara.

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Yayi Taron Sulhu da 'Yan Jam'iyyarsu ta PDP - 4' 35"