Mataimakin Shugaban Hezbollah Ya Shaidawa Isra'ila Cewa Tsagaita Wuta Ce Kawai Mafita

  • VOA Hausa

A portrait of slain Hezbollah leader Hassan Nasrallah sits amids debris at Beirut's southern suburb Rouweiss neighbourhood on October 10, 2024, following overnight Israeli strikes.

A faifan bidiyon da aka nada wanda kuma aka yada a shafukan sada zumunta, ya nuna Qassem yana zaune akan karamin tebur mai dauke da kananan tutocin kasar Lebanon da na Hezbollah da kuma hoton Hassan Nasrallah sabanin yadda aka ganshi a jawabai 2 da ya gabatar tun bayan kisan da aka yiwa Nasarallah.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Hizbullah Na'im Qassem ya gargadi Isra'ila cewa hanya daya ta kawo karshen yakin da ake fafatawa ita ce tsagaita wutar da zata baiwa mazauna yankin arewacin Isra'ila damar komawa gida, inda ya sha alwashin cewa ba za'a yi galaba a kan kungiyar ba.

A faifan bidiyon da aka nada wanda kuma aka yada a shafukan sada zumunta, ya nuna Qassem yana zaune akan karamin tebur mai dauke da kananan tutocin kasar Lebanon da na Hezbollah da kuma hoton Hassan Nasrallah sabanin yadda aka ganshi a jawabai 2 da ya gabatar tun bayan kisan da aka yiwa Nasarallah a ranar 27 ga watan Satumban da ya gabata

Hezbollah ta bude abin da ta kira da fagen taimakawa Gaza daga Lebanon, inda ta kaddamar da kai hare-hare daga kan iyaka zuwa cikin Isra'ila kwana guda bayan da harin da kawarta kungiyar Hamas ta kaiwa Isra'ila hari a ranar 7 ga watan Oktoban bara ya haddasa yaki a zirin gaza.

"Ina shaidawa fagen daga na isra'ila cewar mafita ita ce tsagaita wuta", a cewar qassem a Jawabinsa na 3 tun bayan da wani harin Isra'ila ya hallaka tsohon shugaban kungiyar Hassan Nasarallah.

"Ba ina magana ba ne saboda gazawa, saboda idan Isra'ila bata sha'awar tsagaita wuta, zamu cigaba da fafatawa, a cewarsa.

"Ba za'a yi galaba akan Hezbollah ba, saboda wannan kasarta ce," a cewarsa.