Mata Da Yiyuwar Yin Kuka Idan Babu Sana'a

Turaren Wuta

An bukaci mata dasu tashi tsaye wurin dogaro da kai ta fuskar sana’oi, Aisha Danladi, wata mai sana’ar dogaro da kai ce ta furta haka a hirarsu da wakiliyar DandalinVoa Baraka Bashir.

Tace duk macen da ta ce zata jira a bata lallai tana cikin matsala da yiwuwar yin kuka wata rana muddin bata da sana’ar hannu, tana mai cewa sana’a maganin matsalolin rayuwa, a cewar ta sana’a na magance takaicin zaman duniya.

Ta kara da cewa tana son sana’ar hannunta ya bunkasa sai dai ‘yan matsalar da take fuskanta kamar rashin isassun jari inda take cewa da gwamnati zata taimakawa masu kananan sana’oi lallai da sun inganta harkokinsu na yau da kullum.

Ta ce rashin karfin jarin ya haddasa a koda yaushe sai sun nemi tallafi a wajen ‘yan uwa da zarar jarin ya yi kasa , ta ce a duk lokacin da ta zauna babu sana’a takan ji ba dadi da kuma kasancewa cikin takura.

Aisha ta kara da cewa bata raina sana’a domin kuwa ko a yan kwanaki sai da aka yi mata hanya take karbar zanuwan gado tana sayarwa domin ta samu yar riba da zata kashe bukatun gabanta.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Da Yiyuwar Yin Kuka Idan Babu Sana'a- 2'55"