Hukumar yaki da miyagun kwayoyi watau NDLEA ta jihar Edo tace ta kama kama wani kaya na busasshen ganye wanda ake kyautata zaton cewar tabar we-we ce a cikin wasu kayyakin gini da ake safarar su.
An kama motar me dauke da ganyen na fiye da Naira miliyan 70, a hanyar ta ta zuwa garin Abi dake Jihar Delta daga Akure dake jihar Ondo.
A cewar kwammandan hukumar ta yaki da fataucin miyagun kwayoyi na garin Mr. Wakawa Buba, an daure ganyen ne a jakukuna 409 kuma nauyin su ya kai kilo 7073.
Wadanda ake tuhumama sun hada da Monday Amusoga mai shekaru 39 da Omebu Kingsley, mai shekaru 30, duk ‘yan asalin karamar hukumar Ndokwa ne ta jihar Delta.
Mr. Buba yace hukumar tasu zatayi iyakar bakin kokarinta taga tayi yaki ta mugayyen halayen wadannan mutane a lokacin da yake tabbatar wa da ‘yan sanda kame da kwace kayan da akayi.
“wannan wata sabuwar dabara ce da masu safarar miyagun kwayoyi suka fito da. An jera ganyen tsaf a cikin kayan gini amman munyi nasarar gano ta saboda bayanin sirri da muka samu”
Facebook Forum