Mata da Shiga Badakalar Kudi da Kadarorin Al'umma

Stella Oduah

A da maza aka fi sani da shiga badakalar kudi da kadarorin jama'a Najeriya, amma yanzu lamarin ya sake zani inda mata sun fara shiga.
Da a Najeriya maza aka fi sani da halin muna-muna da yin barna da kudi da kadarorin kasa. To sai dai a 'yan shekarun nan mata ma sun kunno kai wurin shiga badakalar kudi da kadarorin al'umma.

Batun almundahana da karya tattalin arzikin kasa batu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya. A baya can masu rike da mukamiin gwamnati musamman maza suke kan gaba wurin yin almundahana da dukiyar kasa. Amma yanzu su ma mata ba'a barsu baya ba.

Mace ta farko da ta shugabanci majalisar wakilan Najeriya Patricia Eteh ta rasa kujerarta sanadiyar cin hanci da rashawa da yin almundahana da dukiyar kasa. Haka ma an tuhumi Iyabo Obasanjo da ta yi ministar ma'aikatar kiwon lafiya can baya. Ga kuma Cecelia Ibru shugabar bakin Oceanic da ta wawure kudin bankin. Sai kuma Miss Aruma Eteh wadda ita ma aka zargeta da yin muna-muna da kadarorin jama'a. Ta baya bayan nan da aka zarga itace ministar ma'aikatar zirga zirgan jiragen saman Najeriya Stella Oduah da yin almundahana na nera dari biyu da hamsin da biyar.

Suma mata dake aiki a bangarorin masu zaman kansu ba'a barsu a baya ba. Wasu ma da basa aikin ofis suna shiga zargin yin almundahana da kudi da kadarori a lokuta daban daban.

A cikin watan jiya hukumar EFCC ta gurfanar da Iya Gana Ibrahim Bukar ma'aikaciya a Skye Bank a babban kotun tarayya a Abuja bisa zargin ta batar da sawun miliyoyin nera da ba nata ba.

Tsohon manajan banki Malam Ayuba Yahaya ya yi bayani dalilin da ya sa mata na shiga badakalar kudi a bankuna. Ya ce laifin na banki ne domin idan sun dauki mace sai su ce ta je ta samo ajiya ta miliyoyi kaza. Mace zata fita ta yi anfani da kanta ta samo ajiyar amma ba za'a bata komi ba. Don haka zata yi duk abun da zata iya yi ta samu fansa. Shekaru talatin ko ashirin da suka gabata ba'a san mata da cin kudin banki ba.

Hajiya Maryam Sabo shugabar kungiyar lauyoyi mata na kasa da kasa dake kare hakin mata ta dora ma mata laifin kin rikon amana. Ta ce yanzu mata akwai son zujiya. Akwaisu da kwadayin kudi da kuma zubar da mutuncinsu da son a tara abun duniya ko ta halin kaka. Dalili ke nan yanzu mata sun yi watsi da mutuntakarsu. Ta kira mata su ji tsoron Allah.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Da Shiga Badakalar Kudi Da Kadarorin Al'umma - 4:43