Dubban matan kasar Venezuela sun gudanar da gagarumar zanga zangar lumana a kan titunan Caracas, babban birnin kasar ranar Asabar din shekaranjiya don nuna rashin jin dadinsu da dakatar da kuri’ar raba gardama wadda aka so ayi anfani da sakamakonta wajen saukar da shugaba Nicolas Maduro daga kan karagar mulki.
WASHINGTON, DC —
Masu zanga zangar karkashin jagorancin Lilian Tintori da Patricia Gutierrez, matan wasu shahararrun ýan siyasa dake daure kuma sanannu wurin sukar laimirin wannan gwamnati sun tare wata babbar hanyar birnin don nuna rashin jin dadi da kamun-ludayin gwamnatin ta Maduro.
A ranar Alhamis ne jami’an hukumar zaben Venezuela suka dakatar da kuri’ar raba gardamar bayan kimanin shekara guda yan adawa na kyamfen don nuna matsayinsu a kanta.
Jami’an sun ce an gano choge a wurin tattara sunayen masu saka hannu a kan takardun bayyana ra’ayoyi kan wannan shugaban mai ra’ayin akidar gurguzu.