Wata kungiyar rajin kare hakkin bil adamata kasar Syria da mazauninta yake a Birtaniya ta “Syrian Observatory” ta ruwaito cewa sojan sama da na kasa sun koma ga kai farmaki akan garin.
Haka kuma Kungiyar ta Birtaniya tace an samu tashin rigingimun a wurare da dama a inda wannan tsohon birnin tarihi da aka raba shi tsakanin yammacinsa dake hannun gwamnati da kuma gefensa na yamma. Kungiyar tace Rasha da Syria duk sun sake komawa ga hare-haren da suke kaiwa.
Yanzu haka kungiyar ‘yantawayen ta ja kunnen mazauna garin na Aleppo da cewa su nisanci ma’aikatun gwamnati saboda hare-haren da ake jin za’a kaiwa ma’aikatun.
Wannan alma’arin ya tilastawa MDD dakatar da fidda marasa lafiya da tayi niyar yi a ranar Juma’a daga gabashin birnin Aleppo saboda rashin samun tabbacin tsaro daga bangarorin masu fada da junansu.