Masu zanga-zanga a Khartoum suna ci gaba da neman shugaban kasar Omar al-Bashir da yayi murabus, a cigaba da zaman da suke yi a hedkwatar sojan kasar, inda aka ji karar harbin bindiga.
WASHINGTON D.C. —
Akwai rahotonnin dake cewa Jami’an tsaron gwamnati sunyi kokarin tarwatsa taron masu zanga–zangar, wanda ya janyo sojojin suka kare masu zanga-zanga, a cewar wasu da suka shedi abinda ya faru.
Jami'an 'yan sanda sun bayar da tabbacin cewa ba za su taba kaiwa masu zanga zangar hari ba, yayinda dubban mutane ke cigaba da shiga zanga-zangar, a cewar wani dan jarida mai suna Dama da ya zanta da Muryar Amurka.
Duk da cewa tashar telebijin ta Sudan na ci gaba da nuna wasu hotunan bidiyo inda ake ganin wurare kamar ba wasu masu zanga-zanga a ciki, wasu shedu sunce wadanan tsofaffin hotuna ne da aka dade da dauka, ba abinda ke faruwa bane a yanzu.