Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Tayi Kira Ga Kasashen Duniya Su Jawa India Kunne


Firai Ministan Pakistan Imran Khan
Firai Ministan Pakistan Imran Khan

Pakistan a yau Lahadi tayi kashedi ga abokiyar gabanta da take ikirarin tana shirin kaddamar da hari a kanta, lamarin da yasa Pakistan ke kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar matakan diflomasiya domin hana India jefa yankin cikin tashin hankali da rikici.

"Mun tattara bayanan sirri dake tabbatar da cewa India na shirin aiwatar da wani harin soji a kan kasar Pakistan. Akwai yiwuwar kai wannan hari tsakanin ranakun 16 ko 20 ga wannan watan Afrilu", inji ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mehmood Qureshi.

Ya fadawa manema labarai a birnin Multan dake kudancin kasar cewa, Pakistan ta raba sahihin bayanan da ta tattara kuma ta mikasu ga jami’an diflomasiya a Islamabad, daga manyan kasashe masu wakilai na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Qureshi ya nanata cewa, suna so kasashen duniya su san da wannan mummunar dabi’a tare da yin kashedi ga India da yunkurin wuce gona da iri.

A baya Pakistan da India sun yi manyan yake yake guda uku a shekarun 1947, 1965, 1971 da kuma wani takaitaccen fada a shekarar 1999.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG