Irin wannan yanayin ake fuskanta a yawancin cibiyoyin tattara sakamakon zabubukan da aka gudanar ranar Asabar ta gabata.
To sai dai wannan yanayi ko daliba’a ta soke sakamakon zaben a wasu runfuna bai yiwa al’umma dadi ba, ganin yadda suka bata lokaci akan layi kafin su kada kuri’unsu.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar zabe INEC a Sokoto. Shamsuddeen Haliru Sidi, ya ce lallai akwai zabubuka da aka soke saboda wasu dalilai.
Masu jefa kuri'a da suka yi sammako a runfunan zabe, yanzu suke dakon jin sakamakon abin da suka zaba sun nuna damuwa akan wannan lamarin.
Zabuka irin wannan a Najeriya da aka gudanar a baya, wasu lokuta akan sami yamutsi da hayaniya, lamarin da kan ta’azzara har ta kai ga an soke sakamon zaben.
Masanin kimiyar siyasa daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Farfesa Tanko Baba ya ce doka ta tanadi soke zabubuka, saboda wasu dalilai kuma ba za a iya kaddamar da dan takarar da ya samu galaba ba kai tsaye.
Bisa ga yadda lamarin yake yanzu ya sa wasu jama'a na ganin hakan zai zama darasi ga masu zabe akan kaucewa tayar da hatsaniya muddin suna son jin sakamakon abin da suka zaba da wuri.
Ga rahotan Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5