Masu shigar da kara a nan Amurka sun ba mai mujallar National Enquirer rigar kariya

David Pecker mai mujallar National Enquirer mai fallasa duk wani abun kunya da wani babba ya aikata a nan Amurka

Masu shigar da kara a madadin gwamnatin tarayyar Amurka sun ba David Pecker nai mujallar National Enquirer rigar kariya daga duk wani tuhuma bisa ga shaidar da ya bayar akan abun da ya sani game da abun kunyar da shugaba Trumpa aka ce ya aikata

Rahotanni sun ce, masu shigar da kara a matakin gwamnatin tarayya a nan Amurka, sun bai wa wani mutum mai gidan wata mujalla rigar kariya daga duk wata tuhuma, mutumin da ya kasance jigo a binciken da ake yi akan tsohon lauyan shugaba Donald Trump, wato Michael Cohen.

Shugaban kamfanin gidan mujallar National Enquirer, David Pecker, ya hadu da masu shigar da kara, wadanda inda ya zayyana musu alakar da ke tsakaninsa da Cohen da Trump, da kuma wasu kudaden toshiyar baki da aka biya wasu mata biyu, gabanin zaben 2016, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito a rahotonta, wanda ya ambato wasu mutane da ke da masaniya kan wannan badakala.

Saboda irin bayanan da Pecker ya fada a zaman da suka yi da masu shigar da karar, aka ba shi rigar kariyar cewa ba za a tuhume shi da aikata wani laifi ba, a cewar jaridar ta Wall Street Journal.

A farkon makon nan ne, Cohen ya amsa cewa ya aikata laifi, karkashin wata yarejejeniya da aka kulla, bayan da ya zayyana irin rawar da mujallar ta National Enquirer ta taka wajen biyan wata fitacciyar mai shirya fina-finan batsa, Stormy Daniels da wata mata mai suna Karen McDougal, wacce ta yi suna a fannin bayyana a mujallar batsa ta Playboy, domin su yi shiru da bakinsu kan zargin nemansu da ake zargin Trump ya yi ta hanyar lalata.

Wasu takardun kotu, sun nuna yadda shugaban mujallar ta National Enquirer, ya taimaki Trump, domin a kaucewa wallafa labaran batanci akan Trump a lokacin yakin neman zabe.

Shi dai Pecker ya taimaki Trump ne, ta hanyar ganowa tare da sayen labaran abin fallasa na nema-neman mata da ya yi, domin a kaucewa wallafa su a jaridu.