Tsattsamar dangantakar shugaba Donald Trump da kafafen yada labaran Amurka, ta kara fadada a jiya Alhamis, a lokacin da daruruwan jaridun kasar, suka dauki wani mataki na bai-daya domin kare ‘yancin walwalar ‘yan jarida, matakin da ba a taba ganin irinsa ba.
Wannan kamfe martani ne ga sukar da Trump ke yawan yi ma kafafen yada labaran kasar.
Akalla jaridu 350 daban-daban a sassan kasar, aka shirya za su wallafa sharhi daban-daban na nuna goyon bayan muhimmancin walwalar ‘yan jarida da karfin da suke da shi.
Matakin da jaridun suka dauka, na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Trump yake yawan zargin kafafen yada labarai babu kakkautawa, kan cewa suna yada “labaran bogi”, inda kamfen din ya musanta ikirarin da Trump din ke yi na cewa “su ne makiyan al’umar Amurka.”
A jiya Alhamis, Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “kafafen yada labarai masu yada labaran bogi, sune jam’iyyar adawa.”
Facebook Forum