Wannan mataki da hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya wato NBC ta dauka ya biyo bayan gabatar da wani shiri na Idon Mikiya a ranar 5 ga watan Janairu da ya gabata wanda ya tabo batutuwa ciki har da nadin mukamai a hukumar tattara bayanan Sirri ta kasa wato NIA, da a cewar ta an saba wa tsarin mulki na Najeriya sashe na 39 sakin sashe na 3 (ba), wanda ya takaita magana akan abubuwan da suka shafi hukumomin tsaron kasar.
To sai dai a cewar daya daga cikin manyan mahukuntan kafar ta VISION da Farin Wata, Shu'aibu Mungadi, hakan bai zo masu da mamaki ba gannin yadda shirin ke bankado kurakuren gwamnati kuma ga lokacin babban zaben kasar na karatowa
Idan ana iya tunawa, ko a shekarar 2014 sai da gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ta hana gidan radiyon gabatar da shirin, wanda matakin gwamnati mai mulki na yanzu ke nufin sau biyu kenan ana daukar irin wannan mataki kan gidan rediyon, na dakatar da shirin tsawon wata shida tare kuma da cin tarar hukumar rediyon naira miliyan biyar.
Shahararren shirin na Idon Mikiya dai ya samu karbuwa musamman a yankin arewacin Najeriya inda wasu ke buga shi a faifan CD, wanda manyan ‘yan jaridu da masu gidan rediyon Vision FM daga Abuja ke gabatarwa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5