Cibiyar wayar da kan jama’a game da al’amuran addinin musulunci da tattaunawa tsakanin mabiya addinai ta Jami’ar Bayero Kano da kuma ofishin Najeriya na Cibiyar nazarin akidun musulinci ta kasa da kasa kana da tallafin gwamnatin Kano ne suka shirya taron.
Alakar tattalin arziki da zaman lafiya da kuma fatara da talauci na daga cikin batutuwan da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya tabo a jawabin sa wurin bude taron.
Ya bayyana cewa, nahiyoyin duniya sun rabu kashi 2, wato nahiyar masu Watada data matalauta, inda shekaru 30-40 da suka shude masu wadatar ke samun tsaninin arziki, yayin da kuma fatara ke kara tsanin a yankunan kasashe masu talauci, kamar kasashen yankin sahara.
Bisa ga cewar Mai Martaba Sarkin Kano, akwai alaka ta kud da kud tsakanin rashin daidaito ta fuskar tattalin arziki , zamnatakewa da kuma rigingimun siyasa ko akasin haka.
“Ba zai yuwu mu raba rashin zaman lafiya da tattauna al’amuran da suka shafi ci gaba da kuma sha’anin fatara da talauci.”
A jawabin sa, shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki wanda mashawarcin sa kan lamuran tsaro Majo Janar Sale Maina ya wakilta, ya tabbatar da goyon bayan majalisar ga batutuwan da taron zai fito dasu.
Kwararru kan lamuran tsaro da manazarta a fannin daga kasashen Burataniya da Amurka da wasu kasashen Afrika ne ke halatar taron da za’a kammala a ranar alhamis din nan.
Saurari cikakken Rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5