WASHINGTON, D.C —
Al’amura sun fara daidaituwa bayan rikicin da ya nemi kunno kai a Jihar Filato, bayan kashe wasu mutane 15 yan bindiga sukayi a Rukuba Road dake cikin garin Jos.
Duk da kone konen ababen hawa da ofishin Yan sanda da wasu matasa sukayi a jiya, a yau Jama’a sun bude wuraren kasuwancinsu gami da gudanar da harkokin su kamar kullum.
Jami’an tsaro a Jihar sun ce sun shawo kan lamarin. Ga Zainab Babaji dauke da cikakken rahoton.
Facebook Forum