ACCRA, GHANA - Masu ruwa da tsaki a harkar noman shikafa a yammacin Afirka sun gudanar da taron daukan matakan yadda za’a rage shigowa da shinkafar kasashen waje zuwa yankunan Afirka.
Yayin jawabinsa, babban daraktan ma’aikatar abinci da noma a Ghana, Robert Ankobiah a wajen taron masu ruwa da tsaki da kuma kaddamar da dandalin gasar shinkafar Afrika a Ghana, ya ce amfani da shinkafar gida, zai taimaka wajen rage yawan kudin shigowa da shinkafa daga kasashen waje.
Ya kara da cewa, da kyar za a iya bambanta shinkafar ta gida da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje.
Shugaban dandalin gasar shinkafa ta Ghana wanda shi ne shugaban kungiyar Rice Millers ta Ghana, Yaw Adu Poku, ya ce abubuwan da ake noma da su ba wani abin a zo a gani ba ne, don haka farashinmu yake ƙaruwa har ma sama da waɗanda ake shigo da su don haka ba a samun amfanin gona yadda ya kamata.
A nata bangaren, babbar Kwamishinar Birtaniya a Ghana, HE. Harriet Thompson, ta ce gwamnatin Birtaniya ta kuduri aniyar tallafawa harkokin noma a cikin gida da kasuwanci a yankin da kuma noman shinkafa a cikin gida a yammacin Afirka.
Saurari cikakken rahoto daga Hawawu AbdulKarim:
Your browser doesn’t support HTML5