Masu Rajin Kare Yanci A Ukraine Sun Fasa Tagar Wani Banki

‘Yan rajin kare yanci kasar Ukraine sun yi jifa har suka fasa tagar wani Banki dake tsakiyar birnin Kyiv a jiya Asabar.

Sunyi hakan ne domin bikin tunawa da zanga-zangar da ta ture gwamnatin shugaban kasar mai goyon bayan Rasha.

A wannan ranar ce daruruwan mutane suka taru a dandalin dake babban birnin kasar domin tuna ranar ture wannan shugaban, masu zanga-zangar sun kaiwa wasu Bankuna mallakar kasar Rasha dake cikin kasar hari.Yin haka ko ya haifar da cunkoson motoci.

Rahotonnin daga kafofin yada labarai na cikin gida na kasar sun bayyana cewa duk da kokarin da ‘yan sanda suka yi na ganin sun fatattaki masu zanga-zanga amma hakan bai cimma nasara ba.

A ranar 20 ga watan fabarairu na shekarar 2014 an kashe masu zanga-zanga har sama da 100, da yawan su kuma an kashe su ne ta harbin su da bindiga.

Jami'an tsaro ne masu biyayya ga shugaba Viktor Yanukovych sune suka aikata wannan danyen aikin lokacin da suka yi kokarin ganin sun kwantar da tarzomar da ta tura babban birnin kasar cikin rudu da damuwa na tsawon makonni.

Sai dai abinda ya kara harzuka masu wannan zanga-zangar shine ba wani yunkurin ganin an gano wadanda suka yi wannan kissan balle ma ace za a hukunta su kawo yanzu ba wanda zaice ga wadanda suka aikata kissan wadannan mutanen.

Sai dai kashe wadannan mutanen a kasar ta Ukraine ana ganin shine abinda yasa Yunukovych tilas ya bar karagar mulki.