WASHINGTON D.C —
A yayin da ya rage saura sa'oi kadan a fara gudanar da kada kuri'un zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a jamhuriyar Nijer, matasa 'yan kasar dake zama a wasu kasashe daban dabam irin su jamhuriyar Kamaru, da Nijeriya sun ce a shirye suke domin kada nasu kuri'un.
Koda shike rahotanni daga jam'huriyar Kamaru sun bayyana cewa sun bayyana cewa an sami tangarda wajan rarraba katunan zaben domin da dama sun zo masu babu adireshi wasu kuma babu suna sai dai adireshi.
A kwai 'yan Nijer kusam miliyan biyu dake zama a jamhuriyar Kamaru, kuma da dama sun koma kasar domin nuna goyon bayan su.
Ga cikakkiyar hirar..