Masu Neman Takarar Shugaban Kasa a Jam'iyyar Democrat Sun Yi Wata Muhara

‘Yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Democrat su 6 sun gwabza a wata muhara mai zafi da suka yi a jiya Laraba da dare, inda abokan neman takarar Micheal Bloomberg, hamshakin attajiri kuma tsohon magajin garin birnin New York suka sa shi gaba da tambayoyi a karawar ido-da-ido ta farko da suka yi.

Ba tare da bata lokaci ba Sanata Bernie Sanders na jihar Vermont da Amy Klobuchar ta jihar Minnesota suka fara caccakar Bloomberg akan yana kokarin sayen tikitin jam’iyyar Democrat ta hanyar kashe kudi dala miliyan dari hudu ($400M) daga aljihunsa a tallace tallacen yakin neman zabe.

Sanata Klobachar ta ce bata tunanin Amurkawa masu jefa kuri’a za su kalli shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican kuma su ce “suna son wani attajiri” kamar Bloomberg, wanda shine mutum na 12 a jerin masu kudin duniya.

Michael Bloomberg

A nasa bayanin, Micheal Bloomberg ya bayyana nasarorin da ya cimma a matsayin dan kasuwa da kuma tsohon magajin garin birnin New York.

Ya ce 'ni mutum ne mai yawan taimaka wa masu bukata, ba gadan kudin na yi ba, amma fadi tashi na yi har na sami kudina kuma ina amfani da su domin in kawar da Donald Trump, shugaban kasa mafi muni da aka taba yi a tarihin Amurka"