Masu Kudi Sun Tallafa a Yaki Da Sauyin Yanayi a Yankin Sahel

Taron masu hannu da shuni da ya gudana a wannan makon a jamhuriyar Nijer domin tattara kudaden yaki da illolin canjin yanayi a yankin sahel, ya samu goyon bayan kudirin kasashen da wasu dubban miliyoyin kudin CFA kafin nan da watanni 6 masu zuwa.

Kwanaki biyu aka shafe ana tafka mahawara da nufin ganar da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, akan bukatar samun hadin kansu a yakin da kasashen yankin sahel ke shirin kaddamarwa da nufin magance illolin canjin yanayi. A cewar ministan kare muhalli a jamhuriyar Nijar, Almoustapha Garba kwalliya ta biya kudin sabuli.

Rashin cika sharudan da aka gindaya a karkashin yarjeniiyoyin kasa da kasa na daga cikin dalilan da ke hanawa kasashe masu tasowa samun tallafin da aka yi musu alkawari, dalili kenan a wannan karon aka kafa wani kwamitin da zai bi diddigin abubuwan da taron ya tsayar inji Kiri Tinao jami’in kungiyar kasashe renon Faransa FRANCOPHONIE.

Yawaitar aiyukan ta’addanci da kwararar matasan yankin sahel zuwa ci rani ta barauniyar hanya na daga cikin matsalolin da ake alakantawa da canjin yanayi, dalili Kenan shugabanin kasashen sahel suka dage da neman mafita.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Baram.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Kudi Sun Tallafa a Yaki Sauyin Yanayi a Yankin Sahel - 2'30"