Masifar Wutar Daji a Yankunan Jihar California

Gobarar daji a jihar California

Babbar wutar dajin nan dake cin yankuna masu yawa a kewayen birnin Los Angeles na jihar California a nan Amurka, yanzu haka an ayyana ta uku a girma a tarihin jihar, da barnar da ta yi wadda tazo dai-dai da gobarar shekarar 2013 ta hanyar kona sama da hekta 800.

Jami’an agajin gaggawa sunce wasu ‘yan kwana-kwana dubu takwas daga sauran jihohi suna California don taimakawa a kashe gobarar dajin, ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu da manyan motocin kashe gobara.

An kiyasta kudaden da aka kashe akan aikin kashe gobarar kusan dala Miliyan 89.

A jiya Asabar ne jami’an ‘yan kwana-kwana suka ce gobarar dajin da aka yiwa lakabi da Thomas fire, wadda ta fara tun farkon watan Disamba, yanzu haka ta kona kusan hecta dubu 105. An shawo kan kashi 40 cikin 100 na wutar, amma jami’ai sunce gine-gine kimanin 18,000 na fuskantar barazana, kuma iska mai karfi na iya haddasa wata gobarar.