Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fada jiya jumaa cewa ba wani rudu ko kuma kumbuya-kumbuya game da matsayin Amurka akan tattaunawa da kasar Koriya ta Arewa.
Tillerson yana Magana ne a wajen wani taro na musammam na kwamitin samar da zaman lafiya na MDD da ya mayar da hankali akan gwajin makami mai linzami da kasar ta Korea ta Arewa tayi a ranar 28 ga watan jiya.
Sakataren yace cikin biyu dai tilas ne ayi guda kodai Korea ta Arewa ta zabi jingine sarrafa makaman ta masu linzami ko kuma taci gaba fuskantar zaman kadaici wanda ke kara tura jamaan ta cikin halin talauci kunci da damuwa.
Babban jami’in Diflomasiyyar na Amurka ya bukaci kasar ta Korea ta Arewa data jingine wannan mummunar mataki data dauka, ta bada kai bori ya hau domin ta shigo cikin sahun ‘yan uwanta sauran kasahen duniya.
Yace kamar yadda ya furta tun farkon wanna satin yace muddin kasar na neman a dakatar da matakin da ake kudirin dauka kanta to sai fa ta jingine tabio’inta na barazana, kafin duk a haye wani teburin sulhu da ita.
Sai dai shi kuma a wuri daya jakadar Korea ta Arewa a MDD, Ja Song Nam yace mallakar makamin nukiliyar da kasar tayi, abu ne da ya zame mata tilas domin kariyar kanta, yace Amurka ce kawai ta haifar da rudani a yankin ruwan na koriya.
Shiko Sakataren MDD Antonio Gutteres shida sauran mutanen da suka yi Magana a wajen taron taron sun bukaci Korea ta Arewan ne data bi umurnin da kwamitin tsaro na MDD ya cimma domin kaucewa wa duk wata tashin tashina.
Facebook Forum